JUMA’A BABBAR RANA Falalarta Da Hukunce-Huukuncenta
Godiya ta tabbata ga Allha (Subahanahu WA Ta’ala). Tsira da Aminci su tabbata ga fiyayyen halitta, Manzo Allha (salallahu Alaihi Wa sallam) da Alayensa da sahabbansa da wadanda suka bi tafarkinsu har zuwa ranar kiyama. Bayan haka: Na yi tunanin rubuta wannan littafi ne saboda da duba da yadda mafi yawan Musulmi suka jahilci girman wannan rana, da abin da ta kunsa na falaloli da darajoji da hukunce-hukunce, wadanda saninsu yana da mutukar amfani ga duk wani Musulmi. Don haka na yi kokarin in ga na fadi mafi yawancin abin daya kamata a sani a takaice, sauran abubuwan kuwa masu zurfi na yi nuni ga mai karatu zuwa ga wuraren da zai same su,