AMFANIN BANKIN MUSULUNCI
FASSARAR HUDUBA DAGA MASALLACIN SHEIK JA'AFAR MAHMUD ADAM, TUDN MURTALA KANO, 30/7/1432=1/7/2011. Dukkan yabo da godiya ta tabbata ga Allah madaukakin sarki, shi ne mafi sanin abin da kowanne dan Adam ke boyewa a zuciyarsa da abinda yake bayyanawa ina gode masa ina jinjina masa. Dukkan salati ya tabbata ga manzon Allah s.a.w shugaban dukkan halitttu gaba daya, wanda shine mai ceton kowa da kowa. Bayan haka yaku jama’a kuji tsoran Allah ku tsoraci dalilan saba masa da azabarsa ku bar abin da Allah yace ku bari matukar dai ku muminai ne. ku bar cin riba don tana daga cikin abin da yake jawo fushin Allah , tana daga cikin manyan laifuka masu halakarwa.