AMFANIN BANKIN MUSULUNCI

FASSARAR HUDUBA DAGA MASALLACIN SHEIK JA'AFAR MAHMUD ADAM, TUDN MURTALA KANO, 30/7/1432=1/7/2011.


Dukkan yabo da godiya ta tabbata ga Allah madaukakin sarki, shi ne mafi sanin abin da kowanne dan Adam ke boyewa a zuciyarsa da abinda yake bayyanawa ina gode masa ina jinjina masa.
Dukkan salati ya tabbata ga manzon Allah s.a.w shugaban dukkan halitttu gaba daya, wanda shine mai ceton kowa da kowa.
Bayan haka yaku jama’a kuji tsoran Allah ku tsoraci dalilan saba masa da azabarsa ku bar abin da Allah yace ku bari matukar dai ku muminai ne. ku bar cin riba don tana daga cikin abin da yake jawo fushin Allah , tana daga cikin manyan laifuka masu halakarwa.

Allah (s.wt) yace ‘Yaku wadanda sukay I imani kuji tsoran Allah kuma ku bar abin day a saura na daga riba matukar dai ku muminai ne idan ba zaku bari ba ku shirya yaki da Allah da Manzonsa . Bakara.
Allah yace” wadanda suke cin riba baza su tashi basai kamar wanda shedan ya shafe shi saboda suna cewa shi cikin ai kamar riba ne. to allah ya halatta ciniki amma ya haramta riba, wanda duk wa’aziyazo masa masa ya kuma bari, toabin day a wuce komai a kansa lamarinsa nag a Allah. Amma wanda ya komawa riba to wadannan sune ‘yan wuta zasu dauwama a cikinta. Allah ya shafe albarka riba ya rubanya albarkar sadaka. Allah baya son dukkan wani kafiri mai sabo bakara.
Assheikh Abdurrahman sa’adu yace; yace Allah ya ambaci Azzulumai maciya riba masu mummunar mu’amala za’ saka musu da irin abin da suka yin a cin riba anan duniyaa wajen neman abincinsu, ranar alkiyma kuma idan zasu tashi daga kabari irin yadda wanda aljani ya shafa yake tashi ta haka zasu rika tashi suna faduwa.Allah ya shiryar damu amin.
Hadisi ya tabbata a muslim. Hadisin jabir yace; “Annabi s.w.a ya tsinewa duk mai cin riba da wanda ya bayar da wanda ya rubuta da mai bada sheda, yace duk daidai suke
MENENE RIBA KUMA MENE NE BAMBANCIN TSAKANIN RIBA DA RIIBA ?
Sheikh Ragim astihani yana cewa riba itace dan abinda ake samu idan an syar da kaya ma’aan dimiyar da ake kasuwanci don ita. Da riba da riiba duk kari ne a kasuwanci don haka ne ma mushrikai suke cewa duk dayana amma akwai bambamci a tsakani musamman ma rihbar fifiko.
BAMBAMCI TSAKANIN RIBA DA RIIBA.
Yadda zamu bambambace kuwa dole ne mu saka kowanne a ama’uni da shari’a ta dora shi don mu gane abubuwan da suke kawo riba guda uku ne.
1. Idan ka bawa wani kudi ya juya, idan an samu riiba ku raba an samu riiba ku raba, shi ake kra mudaraba.
2. Mutum yayi kasuwanci da kansa dukiyarsa yaci riiiba.
3. Mutum ya karbi dukiyar wani ya juya su raba riibar,.
Idan muka duba da kyau za muga cewa akwai bambamci mai fadi tsakanin riba da riiba, don haka ita riba ba a mata wahala, kana kake dorawa mai bashi ko ciniki ka fifita wani akan wani kayan da irinsu daya yayin ciniki. Kamar cinikin dawa da dawa ko fifita wani akan wata. To riba ta shiga.
BAMBAMCI TSAKANIN RIBA DA KUDIN KWADAGO
Ibnu munzur yana cewa. Kudin kwadago shi ne abin da aka baka don kayi wata wahala wato dai ladan aikin da kayi bayan ka gama aka biya ka, kamar magini ko kafinta ko manomi da dai sauransu.
Haka kudin hayar gida ko dako ko ofis duk yana shiga wannan idan muka duba da kyau za muga cewa akwai bambanci sosai tsakanin riba da kudin kwadago wato ladan wahalar kwadago ya halatta amma, ita riba bata halatta ba kamar yadda ya gabata.
Don haka cinikin da mutum yayi aka biya shi babu wanda kya canacnta wannan hakki sai dai wanda ya aikata kamar ma’aikacin gwamnati da yayi aiki bias gaskiya da rikon amana da kula da lokaci da bin dukkan ka’idojin da aka saka to kaga ya cancanci albashinsa don kwadago yayi.
Haka kudin da aka baiwa lauya don kare ka shari’a matukar yayi gaskiya a aikinsa shima dan kawadago nehalak yaci ba riba ba.
SAMAR DA BANKUNAN MUSULUNCI
Rayuwar mu a yau ta kullu da harkokin banki, hart a kai babu wani mai hankali mawadaci da ba zai iya harka da da banki ba, musamman ma a fagen kasuwanci da sana’o I bankunan da muke tare da su a ayu sun jawo wa jama’a da dama arziki da asara to ina mafita?
Mafita itace dole ne a samara da bankunan da zasu kula da duk abin day a zama dole akan su su kuma toshe duk wata kafa ta barna, wadannan bankuna sune na musulunci.
Lallai ne a samara da bankunan musulunci don su tsarkakewa ala’ummar mu dukiyar su daga kazantar riba a cikin wannan kasa tamu Najeria. Dole musulmi su maid a hankali su kan wannan harka, kuma don amfaninsa. Hakan kuwa zai yiwu domin duk bin da ake so akwai shi a hannun musulmi.
Kudin tsarin mulkin kasa bai haramta ba. Saboda haka akwai kalubale a gabans sosai. Abin da ke kara tabbatar da hakan shine wasu kasashe na musulmai datuni suka yi haka. Wato sun bude bankunan musulunci. In har wasu zasu yi to wasu ma zasu iya babu abin da zai hana masulmai a Najeria yayi yunkuri akan banakin musulunci . matukar dai dalilan smar dahis sun cika to dalilin cin nasarar kuwa sun cika. In har bankunan da bana na musulunci ba zasu rike kansu ta kowacce irin hanya to ya kamata na Musulunci suma su bi irin hanyoyin shari’a kamar yaddad suke a rubuce. Hanyoyin da dama wadanda shari’a ta tsara don cin riba na kai tsayar da kuma wadanda ban a kai tsaye bane, kamar su mudaraba da makarada da muja’ara da makamntansu.
Allah ya sakawa gwamnan babban bankin Najeria da alkhari shi kadai ne ya fito yake ta babatun tabbatar da wannan tsari na samar da bankin musulunci a kasan nan a yanzu. Malamai da shugabannnis da ‘yan siyasa dake majalisa sun ja bakunansu sun yi shiru mun kasa tabuka komai ko da na karfafa gwiwa ga wannan bawan Allah. Ya daukake shi ya taimake shi ya kuma kare shi .
MISALAN WASU BANKUNAN MUSULUNCI.
Bankin Musulunci ba sabon Abu bane, domin kasashe da daama ne suka farar aiwatar dashi shekaru masu yawa kamar bankin Nasir Alijtima’I na kasar Misra, wanda aka kafa shi a shekara 1972, bayan an cika ka’idojinsa a shekara 1971 ya fara aikin da jari imanin miliyan goma sha hudu 14,000,00 na Junaihar misri ya shiga fagen tattalin arziki a duniya a shekara ta 1973.
RIIBAR DA WANNAN BANKI YACI
Bayan y agama biyan nauyin da yake kansa ya sami kashi 6% a shekara ta 1973 sannan ta kaishi kashi 9.5% a shekara ta 1975 da 1979 ta karu a shekara ta 1980 har ta kaishi 10% haka nan ya samu kashi 125%a shekarar 1981 a shekera ta 1982 ribar su ta karye ta dawo kashi 11.4%
Idan ka kula a shekara ta 1982 an samu tawaya a cikin riibar da ak samu da ma kuma haka harkar kasuwanci take a Musulunci, akwai riiba da faduwa a akasuwanci.
Awani bangaren kuma bankin yana da ma’aikata mai zaman kanta ta kula da zakka wannan ma’aikata it ace take tara zakka ga dukkan mao son ya bayar da nasa kason, ta hanyar kananan kungiyoyi wadanda suke tara a masallatai da cikin Unguwanni kananansu da manyansu.
Yawan wadannan Kungiyoyi yana karuwa domin tun suna 120 a shekara ta 1973 har suka kai 700 a shekara ta 1979 kamar yadda abin da ake samu ya karu daga Junaiha dubu ashirin da a shekara ta 1973 ya zuwa 531,000 dubu dari biyar da talatin da daya, a shekara ta 1977, yawan masu bada zakka a wannan banki sun kai kimanin dubu ashirimn da uku, (23) a shekara ta 1977
Bankin said a ya rabawa kimanin mutane dubu arba’ain da shida 46,0000 daga wanann abin day a samu. Kamar yadda ya ciyar a wuirare daban-daban kamar makaranta na haddar kur’ani yara da malamansu gwiwa haka kuma sun tashi tsaye wajen gina masallatai da makarantu manya da kanana.
Sun maida hankalinsu wajen gina asibitoci da wuraren koyar da sana’o I wannanya fito a fili karara wajen bayyana irin riibar da fa’idojin da bankin Musulunci ke iya samu idan an kafa shi don gashi wannan cikin ‘yan shekara kadan da kafa shi har ya cimma nasarori da dama ta fuskar bunkasa tattalin arzikin Musulunci wannan kasa misra.
Don haka bankunan musulunci sun zama wajibi a kafa su don ta hanyar sun e kadai za a iya rage ko magance talaucin day a gallabi jama’ar kasar nan.
Allah ka daukaka Musulunci da musulmai, ka kaskantar da kafirci da kafirai, ka yiwa rayuwarmu albarka, ka zaunar da kasarmu lafiya. Allah ka gafarta wa wadanda suka rasa rayukansu a dalilin ambaliyar rowan sama day a shafi mutanen Fagge, da Dakata da sauran wurare. Allah ya mayarwa da wadanda suka rasa dukiyayinsu da mafi alkharin abins da suka rasa. Wasallalahu ala nabiyinia Muhammad(s.a.w).


DAGA DR. IMAM ABDULLAHI SALEH PAKISTAN Phd.

Comments

Popular posts from this blog

JUMA’A BABBAR RANA Falalarta Da Hukunce-Huukuncenta

AL WALA’U WAL BARA’U

WAJABCIN HATTARA DA FITINU