Posts

Showing posts from 2016

WAJABCIN HATTARA DA FITINU

Hudubar Juma'a  Daga Masallacin Sayyidina Abu Huraira Radiyallahu Anhu, Sokoto. An gabatar da ita a ranar jum’ah 16 Ga Muharram 1431H Daga Bakin Dr. Mansur Sokoto BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM Fitina ita ce jarrabawa wadda dan adam yake gamuwa da ita a kodayaushe cikin rayuwa. Wannan jarabawar ga mummuni alheri ce, domin ta kan bayyana matsayin imaninsa da yardarsa ga Allah madaukakin sarki. Allah Ta’ala yana cewa: A.L.M. Shin mutane na tsammanin a kyale su su ce sun yi imani kuma ba a fitine su ba? Hakika mun fitini wadanda suka gabace su, sai fa Allah ya bayyana wadanda suka yi gaskiya kuma ya bayyana makaryata. Suratul Ankabut: 1-3. Jarrabawar

AL WALA’U WAL BARA’U

Fassarar Khudubar Juma'a daga masallacin Abu huraira(R)        An gabatar da ita a ranar juma’a 2 nd  Safar 1432 A.H Daga bakin Dr. Mansor Sokoto BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM Ya al’ummar musulmi! Hudubarmu ta yau tana magana ne a kan wasu akidu guda biyu na musulunci da ake kira  Wala’a  da  Bara’a. Wala’a na nufin son wanda Allah ke son a so, Bara’a kuma tana nufin kin wanda Allah ke son a ki. Abinda aka sani ga mumini shi ne yana son Allah, yana kuma son masoyan Allah; yana kaunar su, yana taimakon su. Haka kuma yana kin duk abin da Allah ke ki da wadanda Allah ke ki da duk wata dabi’a ko aikin da Allah ke ki. Don haka ne Allah ya sifaita su da cewa, ba su tsoron zargin masu zargi a kan sha’anin Allah. Kuma Manzon Allah  Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam  ya sanya wannan akida