WAJABCIN HATTARA DA FITINU

Hudubar Juma'a Daga Masallacin Sayyidina Abu Huraira Radiyallahu Anhu, Sokoto.
An gabatar da ita a ranar jum’ah 16 Ga Muharram 1431H
Daga Bakin Dr. Mansur Sokoto

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

Fitina ita ce jarrabawa wadda dan adam yake gamuwa da ita a kodayaushe cikin rayuwa. Wannan jarabawar ga mummuni alheri ce, domin ta kan bayyana matsayin imaninsa da yardarsa ga Allah madaukakin sarki. Allah Ta’ala yana cewa: A.L.M. Shin mutane na tsammanin a kyale su su ce sun yi imani kuma ba a fitine su ba? Hakika mun fitini wadanda suka gabace su, sai fa Allah ya bayyana wadanda suka yi gaskiya kuma ya bayyana makaryata. Suratul Ankabut: 1-3.
Jarrabawar

da Allah ke yi wa mummuni ta kan fara ne daga cikin gidansa; ga iyalansa; matansa da ‘ya’yansa da dukiyarsa, kamar yadda Allah ya ce: Tabbas, su dai dukiyoyinku da ‘ya’yanku fitina ne gare ku, babbar lada kuwa tana wurin Allah. Don haka, ku ji tsoron Allah iyakar ikon ku, kuma ku ji ku yi da’a, ku yi sadaka da abinda zai zama alheri gare ku. Wanda duk aka kare shi daga rowar rayuwarsa to, wadannan su ne masu rabauta. Suratut Tagabun: 15-16.
Fitina haka ma tana iya zama ga jikin mutum ta hanyar curuta ko wata musiba da ke cim masa. Kamar yadda Allah ya jarabci bawansa Annabi Ayyub Alaihis Salam ko ta hanyar mutuwar da ko mata ko masoyi kamar yadda aka jarabci Annabi Yakub a lokacin da aka batar masa da Yusuf Alahimas Salam. Jayayyar mutum da shaidan wajen kauce ma sabo ita ma fitina ce. Fitinar son zuciya da shawa ga kawace-kawacen duniya ita ma na daga cikin abubuwan da aka jarabci dan adam da su. Alheri da sharri duka suna iya zama fitina ga mutum, amma hakuri a kan sharri da cuta ya fi sauki a kan hakurin fitina ta alheri kamar fitinar kudi da ta mulki da daukaka ta fuskar ilimi ko makamancin haka.
Abin da ake bukata ga mumini a cikin kowace jarrabawa shi ne ya zamo mai hakuri. Hakurin bin Allah, da hakurin barin sabon Allah, da hakurce ma kaddarorin da ba shi da iko a kan su; ya zamo bai yi raki ba. Masu matsayi a cikin jama’a dole ne sai sun yaki shaidan don kada rudi ya shige su, ko girman kai ya kama su, su fara wulakanta mutane, su manta matsayin Allah da ya daukaka su a cikin ganin damar sa.
Allah ya kan kawo fitina ga ilahirin al’umma a wasu lokutta ta hanyar annoba, ko fari, ko tsadar abinci da abubuwan bukata, ko aukuwar rashin fahimta da haifuwar rikici a tsakanin jama’a. Duka wadannan jarabawowi ne da ke bukatar hakuri da sanin abinda ya kamata ga mumini ya yi a irin wannan yanayi.
Masu kira zuwa ga gaskiya a kodayaushe suna cikin fitina dangane da rashin fahimtar manufarsu da kyawon aikinsu. Za a tuhume su da yin barna ko a ce suna da mugunyar manufa, ko sun gurgunta ci gaba. Kamar yadda Fir’auna ya ce: Ku bari in kashe Musa, domin ina gudun ya canza maku addini ko ya bayyanar da fasadi a cikin kasa. Suratu Gafir: 26
Fitinun da suka shafi al’umma a wannan kasa suna da yawa. Ga dai yaduwar talauci, ga yawaitar rashin aikin yi, abin da ya haifar da sace-sace da yawaitar fashi da makami da Areaboism (Ta’addanci na cikin gari). Sai tsadar abinci da abubuwan bukatun rayuwa. Yanzu kuma ga yawaitar tashe-tashen hankula a tsakanin musulmi wadanda suka haifu a dalilin kauce ma karantarwar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam da bin son rayuka da kungiyanci.
Babu abinda zai fitar da mu daga wadannan fitinu da suka dabaibaye mu sai komawa ga littafin Allah da Sunnar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam bisa tafarkin magabata; musulmin farko. Na biyu : Dole ne mu rinka amfanuwa daga tarihi da abubuwan da suka auku ga jama’a can baya kamar irin fitinun da ‘yan Shi’ah suka sha tayarwa a cikin al’ummar musulmi da kungiyar Khawarij da makamantan su, zamu ga cewa babu wanda ya haifar ma al’ummar musulmi da mai ido a cikin su. Na uku: Mu rinka sanya hakuri, mu rage gaggawa koda wajen kawar da barna. Mu duba yadda gaggawar Annabi Musa Alaihis Salam wajen zuwa wurin ubangijinsa ta kawo fitinuwar al’ummarsa da bautar dan maraki. Na hudu : Mu kusanci malaman sunna a kodayaushe don neman shiriya da gaskiya, kada mu dauki ko wane mataki a kowane irin lamari sai da shawarar su.
Karantarwar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam ta nuna cewa, ba a son musulmi ya nemi fitina ko ya tayar da ita. Masu kira zuwa ga gaskiya kuma dole ne su kauce mata iyakar ikonsu, sai idan ta cim ma su bisa ga kaddarar Allah sannan su rungume ta. Muslim ya ruwaito Hadisi daga Anas Radiyallahu Anhu cewa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam ya ziyarci wani marar lafiya wanda ya shiga cikin wani irin mawuyacin hali, sai ya ce masa, wace addu’a kake yi ? Ya ce: Na roki Allah cewa, duk wata azabar da zai yi min ya gaggauto min da ita nan duniya, don in samu sauki a lahira. Sai Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam ya ce masa, to, ai ba ka iyawa. Ka roki Allah ya yi maka sauki duniya da lahira. Sannan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam ya yi masa addu’a ya kuma samu sauki. Haka ma wajen yaki, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam ya karantar da cewa, kada ayi gurin faruwar sa, amma idan ya faru to, a fuskance shi da gaske. Haka ma duk wani bala’i ko jarrabawa an so musulmi ya yi ta rokon Allah tsari daga gare su. Wanda duk ya kira fitina ya fi kowa gudun ta idan ta taso. Wadanda suka fi kowa daraja ma ga abinda Allah ya ce masu : Hakika kun kasance kuna gurin mutuwa (shahada) kafin ku hadu da ita. To, ga ta nan kun gani da idonku kuna kallo. Ali Imran: 143.
Kuskure ne babba musulmi ya yi farin ciki da cewar ‘yan kungiya kaza sun yi tashin hankali an kashe su, ballantana ya yi gurin faruwar haka ga wasu mutane.
Allah ya zaunar da mu lafiya, ya kuranye mana fitinnu da musibbu da bala’oi, ya daukaki gaskiya a kan karya.

Comments

Popular posts from this blog

JUMA’A BABBAR RANA Falalarta Da Hukunce-Huukuncenta

AL WALA’U WAL BARA’U