AL WALA’U WAL BARA’U

Fassarar Khudubar Juma'a daga masallacin Abu huraira(R)       
An gabatar da ita a ranar juma’a 2nd Safar 1432 A.H
Daga bakin Dr. Mansor Sokoto

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
Ya al’ummar musulmi! Hudubarmu ta yau tana magana ne a kan wasu akidu guda biyu na musulunci da ake kira Wala’a da Bara’a.Wala’a na nufin son wanda Allah ke son a so, Bara’a kuma tana nufin kin wanda Allah ke son a ki. Abinda aka sani ga mumini shi ne yana son Allah, yana kuma son masoyan Allah; yana kaunar su, yana taimakon su. Haka kuma yana kin duk abin da Allah ke ki da wadanda Allah ke ki da duk wata dabi’a ko aikin da Allah ke ki. Don haka ne Allah ya sifaita su da cewa, ba su tsoron zargin masu zargi a kan sha’anin Allah. Kuma Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam ya sanya wannan akida
a matsayin matakin koli na imani:
( أوثق عرى الإيمان الموالاة في الله والمعاداة في الله والحب في الله والبغض في الله )
Albani ya inganta shi a cikin Silsilah Sahiha (4/306).
Idan ka ce don me zamu ki kafirai? Amsa ita ce, don su makiyan Allah ne. Kuma mu ma makiyanmu ne. Wannan shi ne abinda Allah ya fada mana a Suratul Mumtahanah:1-2 da kuma Suratu Ali Imran:28.
Wadanda Allah ke so mataki mataki ne, haka su ma wadanda Allah ke ki. Kuma wajibi ne kowa mu ajiye shi a kan matakinsa. Annabawa da manzanni suna sama ga sauran mummunai mutanen kirki. Su kuma mutanen kwarai sun tsere ma masu fajirci koda musulmi ne. Fajirai musulmi sun fi matsayi a wurin Allah da masoyan Allah a kan kafiri kowane iri.
Allah ya kira kafirai najasa. Suratut Taubah: 28.
Ya ce su azzalumai ne. Suratul Bakarah: 254.
Sannan mayaudara ne, ba su cika ma musulmi alkawali. Suratut Taubah: 1-10.
Kuma a kullun cikin kashe kudi su ke don su gurgunta addinin Allah, su ga bayansa. Suratul Furkan: 55 da kuma Suratul Anfal: 36
Kuma suna muguwar fata gare mu cewa mu kafirta irin su. Kuma zasu yi duk iya abinda zasu iya don cimma wanna kazamar manufa tasu. Suratun Nisa’i: 89, da Suratul Bakarah: 109 da 218.
Allah Ta’ala kuma ya ce, su ba su kaunar mu koda mun kaunace su sai dai su yi mana kissa, a cikin haka kuma suna kulle-kulle don ganin sun ruguza al’amarinmu. Suratu Ali Imran: 118-120.
Mu yi tunanin abinda Allah ya fada game da Banu Isra’ila cewa, rashin imani ne ya sa su son makiyan Allah. Suratul Ma’ida: 80-81.
Madaukakin sarki ya katse duk wani hanzari da musulmi zai bayar wanda yake sa ya jibinci wani kafiri makiyin Allah. Ga abinda ya ce a cikin Suratul Ma’ida:
Ya ku wadanda suka yi imani! Kada ku riki Yahudu da Kirista a matsayin masoya. Sashensu na kaunar sashe. Kuma duk wanda ya jibince su cikinku to fa hakika yana cikin su. Tabbas, Allah ba ya shiryar da mutane azzalumai. Zaka ga masu ciwo a cikin zukatansu suna gaggawar shiga cikin su, suna cewa muna tsoron matsala ta same mu. To, ai Allah ya kusa ya kawo nasara ko kuma wani al’amari daga wurinsa sai su wayi gari suna masu da-na-sani a kan abinda suka boye a cikin zukatansu. Suratul Ma’ida: 52.
Haka kuma Allah ya hane mu mu kaunace su kome karfin dangartakar mu da su:
Ba zaka samu wasu mutane da suka yi imani da Allah da ranar lahira ba suna soyayya da wanda ya ki Allah da manzonsa koda kuwa ubannensu ne ko ‘yan uwansu ko danginsu. Wadancan su ne wadanda Allah ya rubuta imani a cikin zukatansu kuma ya karfafa su da wani Ruhi daga wurinsa kuma yana shigar da su gidajen aljannar da koramu ke gudana a cikinsu suna masu dawwama a cikin su. Allah ya yarda da su, kuma sun yarda da Allah. Wadancan su ne rundunar Allah. Ku saurara! Hakika, rundunar Allah su ne masu rabauta. Suratul Mujadilah: 22.
Sahabban Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam sun tarbiyyantu a kan wadannan ayoyi da muka karanta shi ya sa rayuwarsu ta zamo tsantsa saboda Allah. Kuma duk wanda ke kin Allah to, sun kama gaba da shi kenan ila yaumil kiyamati. Tarihi ya tabbatar da wannan. A ranar Badar misali, Sayyidina Abubakar Siddik ya kira dansa na cikinsa don su yi mubaraza, kuma ya ce da ya fito tabbas da na kashe makiyin Allah. Amru bin al Ass shi kuma kawunsa ya kashe Asi bin Hisham. Su kuma Ali da Hamza sun kashe danginsu Utbatu da Shaibatu. A ranar Uhud Abu Ubaida bin Al Jarrah shi ya kashe mahaifinsa. Mus’ab bin Umair shi ya kashe kaninsa Ubaidu. A lokacin da Abdullahi dan Ubayyu ya taba mutuncin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam da kyar ya sha daga hannun dansa wanda ya tashi kashe shi ba don Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam ya hana shi ba.
Mujaddidi Usmanu (Allah ya kara masa rahama) ya bayyana muhimmancin wannan akida inda ya wallafa wani littafi akan ta, ya sa masa suna Kitabul Amri bi muwalatil muminin wan nahyi an muwalatil kafirin. Duk ayoyin nan da muka kawo Shehu ya kafa hujja da su yana mai cewa, babu sassafci ko kadan a cikin wannan lamari. Da haka shi ma ya gina al’ummar da ta kafa daular musulunci a wannan kasa.
Ya ku al’ummar musulmi! Tarihi ya tabbatar da cewa, babu wata akida wadda ta taimaki musulmi wajen kafa addinin musulunci kamar wannan akida ta Wala’a da Bara’a. Sanin haka shi ya sa Tattar na wannan zamani suke ta kai da komo a cikin kasashen musulmi – musamman na larabawa – suna neman a cire wannan babi daga manhajar karatun yara.
Haka kuma tarihi ya tabbatar da cewa, babu sadda musulmi suka gamu da matsala ga rayuwarsu kamar lokacin da suka yi biris da wannan akida. Mu karanta labarin Muhadirud Daula, wani kirista da ya samu matsayi a zamanin gwamnatin sarki Al Malik As Salihwanda saboda irin matsayin da yake da shi da mike kafafu a kasar musulmi sai da ya kai ga sa wani kirista da ya musulunta ya koma ga addininsa. Wannan mutum ya wulakanta musulmi matuka, musamman kuma malamai. Haka kuma an ce a gidansa kullum akwai baki daga kasashen waje wadanda ba musulmi ba. Kai, daga karshe dai shi ne ya jawo Faransawa ya taimaka ma su suka ci musulmi da yaki bayan duk amincewar da musulmi suka yi ma sa. Wannan tarihi ya maimaitu a lokutta da dama. Duk sadda musulmi suka amince ma kafiri, suka kyautata ma sa zato, ko suka dauke shi wawa wanda bai san abinda yake ba, to, sai sun dandana kudarsu a hannunsa.
Wannan shi ne abinda ya faru kuma yake faruwa a wannan kasa tamu. Daga gidan kaso musulmi ‘yan arewacin kasar nan suka je suka dauko wani criminal wanda ke jiran hukuncin kisa. Suka wanke shi daga laifinsa. Suka gyara ma ‘yan Najeriya shi. Suka yi masa kanfe. Suka ba shi kudi da duk kayan aikin da yake bukata, suka maida shi shugaban wannan kasa. Ba su yi wannan don Allah ba, ba su yi don ci gaban wannan al’umma ba. Sun yi haka ne don nasu bukatun na kashin kansu. Sai Allah Ta’ala ya tabbatar da gaskiyar maganarsa. Wannan mutum ya zame ma najeriya da ‘yan najeriya kaya, musamman ma dai musulmi. Da kyar da addu’oi Allah ya gwada mana baya gare shi. Su kuma wadannan da suka yi masa wannan gata, sai ya wayi gari ba shi da makiyi; abokin gaba da adawa irin su.
To, a yau ma wancan kuskuren da wadancan suka yi shi wasu ke son su sake maimatawa. Ba zasu yi wannan don suna tunanin wani alheri ga kasa ko ‘yan kasa ba. Ba zasu yi haka don suna son zaman lafiya ko ci gaban jama’a ba. A’a, su dai suna da wasu bukatu na kashin kansu da suke son biya ta hanyar yin haka.
Wannan mutum dai tashin farko ya nuna mana ko shi wane ne. Ya fara da kwashe rijiyoyin mai guda tara na wannan kasa ya mallaka ma jaharsa. Ya wanke ‘yan uwansa daga ta’addancin da su da kansu suka yi ikirarin sun yi shi. Ya tsayar da wani kataferen project na gyara tattalin arzikin arewa wanda marigayi Umaru Musa ya basuwa. Kafin haka wannan project Gen. Abdussalami ne ya bada shi, Obasanjo ya soke. Wannan fa ba a yi zabe aka tabbatar da wannan mutumin ba kenan. To, ina ga ya kama tenure ta kansa?!
Muna tunatar da al’ummar musulmi da dukkan wadanda abin ya shafa cewa, wannan lamari fa akida ne. Kuma wanda bai ji maganar Allah ba lalle ne zai ji ta shaidan. Don haka wajibi ne ga duk wanda ke da iko ga tsayar da ‘yan takara ya tabbata ba shi da hannu ga dora kafirci a kan musulunci. Idan ta dawo tsakanin musulmi da musulmi kuma wajibi ne a kamanta neman mai dama-dama wanda ake sa ran samun gyara da ci gaba a karkashin mulkinsa. Mu nemi gyara tun yanzu don kanmu da diyanmu da suke tafe a bayanmu. Mu tuna, abubuwa ukku su ne jigon rayuwar wannan kasa: Na farko Ilmi, Na biyu arziki, Na uku shugabanci. Biyu na farko mun riga mun rasa su. Idan muka yi sakaci da ukkun to ba abinda za a ce sai La haula Wa la kuwwata illa billah.
Abinda ya faru ga wasu kasashen Afrika ya kamata ya zama darasi a gare mu. Ga Benin nan wadda a da ake kira Dahomey. Kasa ce ta musulmi da a yanzu tana son ta yi mu su kanshin dan goma. Wannan shi ne abin da ya faru a kasar Cameroon bayan kuren da Alhaji Ahmad Ahidjo ya tabka na amince ma mataimakinsa wanda Allah ya ce kada a amince ma. Halin da Ruwanda take ciki shi ma wani darasi ne. Haka Ghana da Cote d’iboire da Djibuti da sauran su. Me ya sa ma zamu je nesa? Abinda yake faruwa a Jos kawai ya ishe mu. Duk wadannan wurare da muka zana na musulmi ne tun can asali amma saboda sakaci da amince ma wadanda Allah ya ce su mayaudara ne sai ganwo ya jirkice ma dame. Saboda haka, yana da kyau mu farka tun lokacin nadama bai zo ba.
A karshe muna kira daga wannan mimbari zuwa ga duk musulmin kasar nan cewa, su yi rajista don shirin zabe wadda za a yi daga 15 zuwa 29 ga wannan wata na Janairu da muke cikin sa. Haka ma su bari duk iyalansu maza da mata wadanda suka cika shekarun da ake nema su ma su yi rajista. Domin ka’idar musulunci ita ce, yaki yana zama wajibi ga musulmi idan aka kawo hari cikin gida a kan kowa da kowa; namiji da macce ba a dauke ma kowa. A halin da muke ciki kuwa an riga an kawo mana hari har kuryar daki. Don haka dole ne mu tashi tsaye. Ya Allah! Ka taimake mu. Allah ka yi muna dace, ka dibarta mana; kada ka bar mu da dibarar kawunanmu.

Comments

Popular posts from this blog

JUMA’A BABBAR RANA Falalarta Da Hukunce-Huukuncenta

WAJABCIN HATTARA DA FITINU