WAJABCIN HATTARA DA FITINU
Hudubar Juma'a Daga Masallacin Sayyidina Abu Huraira Radiyallahu Anhu, Sokoto. An gabatar da ita a ranar jum’ah 16 Ga Muharram 1431H Daga Bakin Dr. Mansur Sokoto BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM Fitina ita ce jarrabawa wadda dan adam yake gamuwa da ita a kodayaushe cikin rayuwa. Wannan jarabawar ga mummuni alheri ce, domin ta kan bayyana matsayin imaninsa da yardarsa ga Allah madaukakin sarki. Allah Ta’ala yana cewa: A.L.M. Shin mutane na tsammanin a kyale su su ce sun yi imani kuma ba a fitine su ba? Hakika mun fitini wadanda suka gabace su, sai fa Allah ya bayyana wadanda suka yi gaskiya kuma ya bayyana makaryata. Suratul Ankabut: 1-3. Jarrabawar